Labarai
Amfani da fasahar zamani na da alfanu ga kasuwanci- Barista Ibrahim Mukhtar
Ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci da masana’antu da ma’adanai a jihar Kano ta bukaci ‘yan kasuwa da su rungumi tsarin fasahar zamani kamar yadda takwarorin su na kudancin kasar nan ke yi, domin bunkasa harkokin kasuwancin su.
Shugaban Ma’aikatar Barista Ibrahim Mukhtar, shi ne ya bayyan bukatar jiya yayin bikin rantsar da sabbin shugabanin kungiyar ‘yan kasuwa ta Galadima.
Barista Ibrahim Mukhtar ya kuma yi kira ga sabon shugaban da ya kwatanta adalci a tsakanin wadanda yake mulka, don samarwa kasuwar cigaba.
A nasa jawabin sabon shugaban kungiyar ‘yan kasuwar ta Galadima, Mustapha Shuaibu Sule, ya ce zai yi duk mai yiwu wa wajen hada kan ‘yan kasuwar tare da kawo mafita ga matsalolin da suka addabeta.
Wanda ya ce ‘zasu duba kalubalen da kasuwar tasu take fuskanta, tare da maganceta, don samarwa kasuwar cigaba mai dorewa’.
A yayin bikin rantsarwar kwamishinan ya bada kyautar injin gasa kilishi mai amfani da lantarki ga kungiyar mahauta ta kasuwar Singa.
Rahoton: Muhammad Sani Uba
You must be logged in to post a comment Login