Labarai
Za mu bibiyi Miliyan 100 din da Gwamnatin Kano ta yi mana alkawari-Gamayyar ‘yan Kasuwa

Gamayyar shugabancin kungiyar ‘yan kasuwar jihar Kano ta sha alwashin taimakawa tare da farfado da Kasuwancin ‘yan kasuwar rukunin masu kananan masana’antu na yankin Dakata wadana iftila’in gobara ya shafe su a kwanakin baya.
Jagorancin kungiyar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da Ido na asarar da aka samu wajen tare da bada tallafi don rage radadi ga ‘yan Kasuwar.
Da ya ke jawabi, shugaban gamayyar ‘yan kasuwar ta jihar Kano, Alhaji Sabi’u Bako, ya ce za su bibiya tare da tabbatar da cewar an bada naira Miliyan 100 da Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin bai wa ‘yan Kasuwar.
A nasa jawabin shugaban kungiyar masu kananan masana’antu ta kasa NAKSI, reshen Kano Alhaji Aminu Ibrahim Kurawa, ya bukaci jagororin kasuwanni da su hada kai tare da yin duk mai yiwuwa wajen ganin an tallafa wa wadanda suka yi asarar dukiyoyin su sakamakon gobabrar.
You must be logged in to post a comment Login