Labarai
Amnesty ta bukaci a gaggauta yin bincike kan harin da jirgin sojoji ya kai wa jami’an Sa kai

Kungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International, ta bukaci a gaggauta gudanar da bincike kan hari ta sama da dakarun soji suka kai a ƙauyukan Maraya da Wabi a ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara, inda aka kashe mutane 20 tare da jikkata wasu da dama.
Wannan na cikin sanarwar da Amnesty ta wallafa a shafinta na Facebook a Litinin din makon nan.
Sanarwar ta bayyana cewa mutanen da harin ya ritsa da su jami’an sa kai ne da suka taru domin kare ƙauyukansu daga hare-haren ’yan bindiga.
Amnesty ta ce ko a watan Janairu, irin wannan hari ya hallaka yan sa kai 16 a Tungar Kara da ke ƙaramar hukumar Maradun a jihar Zamfaran.
Kungiyar ta bayyana cewa irin waɗannan hare-hare da ake kaiwa da jiragen yaki, tare da kashe fararen hula da dama, babbar matsala ce ta take haƙƙin ɗan adam.
Ta kuma buƙaci hukumomi su gudanar da bincike cikin gaskiya, domin hukunta waɗanda ke da alhakin aufuwar lamarin.
You must be logged in to post a comment Login