Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

An ƙaddamar da makarantar da iyalan marigayi Magaji Ɗanbatta suka buɗe

Published

on

Iyalan ɗaya daga cikin Dattawan da suka kafa jam’iyyar siyasa ta Nepu a shekarar 1950, Alhaji Magaji Danbatta, sun gina makarantar Naziri da Firamare ga al’umma.

A ranar Asabar ne aka ƙaddamar da makarantar a garin Ɗanbatta a wani taro da ya samu halartar al’ummar gari da masu ruwa da tsaki.

Hajiya Amina Magaji Ɗanbatta ita ta assasa ginin kafin daga baya sauran ƴan uwanta suka bada gudunmawa.

Ta ce “Makarantar ta yi daidai da zamani kuma an gina ta domin ƴaƴan marasa shi”.

Ta ce “Makarantar tana da ajujuwa guda 8 da Ofishin Malamai da na shugaban makaranta da banɗakuna na zamani da kuma wadataccen fili”.

Al’ummar garin sun bayyana farin cikin su, da samar da makarantar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!