Labaran Kano
An bukaci ‘yan kasuwa da su sabunta lasisinsu
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci ‘yan kasuwar hantsi ta Dawanau da su cigaba da bin ka’idojin da ma’aikatar gona ta shimfida musu wajen gudanar da kasuwancin su.
Kwamishinan ma’aikatar gona ta jihar Kano Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna ne ya bayyana hakan, yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki na kasuwar da aka gudanar a dakin taro na ma’aikatar.
Kwamishinan da ya samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar gona Alhaji Adamu Abdu Faragai, ya ce, shakka babu yan kasuwar na taimakawa ta bangaren cigaban tattalin arziki, sannan ya bukacesu da su rubanya.
Wannan dai na cikin wata sanarwa da jam’in yada labaran ma’aikatar gona Hafizu Lawan ya sanyawa hannu.
Ta cikin sanarwar, babban sakataren ya ja hankalin yan kasuwar da suyi dukkan mai yiwuwa wajen sabunta lasisin yin kasuwancin su, don gabatar da harkokin su bisa doka duba da cewa ma’aikatar za ta dauki matakan da Suka kamata kan ‘yan kasuwar da basu da lasisin gudanarwa.