Labarai
An ceto masu ibada 38 na Kwara tare da kuɓutar da ɗalibai 51 na Neja- Shugaban Tinubu

Shugaban kasa Bola Tinubu, ya sanar da ceto masu ibada 38 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a cocin Eruku da ke jihar Kwara.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, shugaba Tinubu, ya kuma tabbatar da kuɓutar ɗalibai 51 cikin 315 da aka sace a jihar Neja, Sai dai ba yi ƙarin bayani ba kan yadda aka ceto su ba.
Ya kuma nanata cewa “Ina ci gaba da bin halin da ake ciki kan yanayin tsaro a ƙasa baki ɗaya kuma ana ba ni bayanai akai-akai daga inda abubuwan ke faruwa,” in ji shi.
“Haka nan, ina mai farin ciki cewa an gano 51 daga cikin ɗaliban makarantar Catholic School ta jihar Neja.”
Tun da farko, ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya ta ce ɗaliban sun gudu ne daga hannun masu garkuwar tsakanin Juma’a da Asabar bayan sace su ranar Alhamis da dare.
You must be logged in to post a comment Login