Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An gano maboyar yan bindiga a Tsafe ta jihar Zamfara

Published

on

Rahotanni daga karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara sun tabbatar da cewa a yanzu an gano maboyar yan bindiga a yankin.

Shugaban karamar hukumar ta Tsafe Alhaji Aminu Mudi Tsafe ne ya tabbatar da hakan a zantawarsa da wakiliyar Freedom Radio Fatima Muhammad Adamu.

“Lokacin da yan bingiga suka kai hari a jiya Lahadi, jami’an soji sun bi bayan su, inda a nan ne suka gano maboyar ta su”.

“Sanin maboyar ta su zai taimaka mana wajen farmarkar su tare da lalata maboyar ta su, kuma tuni jami’an tsaro sun fara shirin tunkarar su” a cewar Mudi Tsafe.

A ranar Lahadi ne wasu yan bindiga suka kai hari karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara tare da kashe mutane da dama ciki har da dan gidan tsohon mataimakin sifeton janar na yan sanda Mamman Tsafe.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!