An Tashi Lafiya
An gudanar da taron bita ga ‘yan Jarida da kuma ƙungiyoyin masu zaman kansu anan Kano
An gudanar da wannan taro ne da haɗin gwiwar cibiyar CAJA mai rajin tabbatar da adalci da shugabanci na gari.
Hukumar ƙwadago ta duniya ta ce, zata ƙara ƙaimi wajen tabbatar da ƴanci da kuma walwalar ma’aikata a ƙasashen duniya.
Babban jami’in hukumar a nan Najeriya Austin Erameh ne ya bayyana hakan a nan Kano, yayin wani taron yini biyu da hukumar ta shirya ga ƴan jarida da ƙungiyoyi masu zaman kansu.
Taron mai taken “Media Toolkit” ya horar da ƴan jaridar kan yadda za su riƙa zaƙulo labaran da ya shafi haƙƙoƙin ma’aikata.
Ya kuma yi ƙarin bayani cewa “Ashekarar 2020 hukumar kwadago ta duniya ILO ta samar da wani kunshi mai suna Media Toolkit wanda zai rinka wayar da kan yan jaridu a duk duniya akan hanyoyin da zasu bi domin zakulo labarai da suka shafi kwadago da wahalhalun da maaikata ke samun kansu aciki, a wuraren ayyukan su ko kuma yayin neman aiki.
Hukumar ta bukaci Kasashe da dama da su samar da irin wannan wayar da kan. A shekarar 2020 ne, hukumar ta ILO ta fara aiki da wannan tsari na wayar da kan yan jaridu da kuma kungiyoyi masu zaman kansu, akan yadda zasu inganta hanyoyin samun labaran da suka shafi rashin jin dadin maaikata da kuma wahalhalun samun aiki.”
Kwamared Kabiru Sa’id Dakata shine shugaban cibiyar. Yace babu shakka bitar ta taimaka matuƙa, domin mahalarta horon sun ƙara sanin dokokin ƙasar nan dama na ƙasa da ƙasa wadda Najeriya ta rattabawa hannu, da kuma yadda za’a rage mummunan halin da mutane suke ciki da hanyoyin za’a bi don a rage safarar mutane.
You must be logged in to post a comment Login