Labarai
An kama wanda ake zargi da sace mota a gidan gwamnatin Kano

Ana zargin ɗaya daga cikin direbobin gidan gwamnatin Kano, da satar wata mota kirra Toyota Hilux da ake amfani da ita a ayarin mataimakin gwamnan jihar Kano.
Sai dai wasu bayanan sirri da Freedom Radio ta samu, sun tabbatar mata da cewa, an samu nasarar kama wanda ake zargi da satar motar wanda guda ne cikin direbobin fadar gwamnatin ta Kano.
Bayanan sun bayyana cewa, jami’an tsaron gidan gwamnatin sun cafke wanda ake zargi da sace motar mai suna Ya’u Gezawa a jiya Talata inda har ya ke hannun jami’an.
You must be logged in to post a comment Login