Labarai
An kammala binne gawar marigayi Buhari

An kammala binne gawar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura na jihar Katsina da misalin ƙarfe 5:50 na yamma.
A ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli ne Muhammadu Buhari ya rasu a birnin Landan na Birtaniya bayan shafe dogon lokaci yana jinya.
Marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya rasu ne ya na da shekara 82 a duniya, shekara biyu bayan sauka daga muƙamin shugaban ƙasa.
Kafar yaɗa labarai BBC ta ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya rasu ya bar mata ɗaya A’isha Buhari da Kuma ƴaƴa 10.
You must be logged in to post a comment Login