Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An kashe barayin shanu da masu garkuwa da mutane a Katsina

Published

on

Rundunar yan sandan jihar Katsina, ta yi nasarar kashe wasu ‘yan fashi da kuma masu garkuwa da mutane da suka addabi Kananan  hukumomin  Kankara da Dan Musa.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yansandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya sakawa hannu ta tabbatar da cewar, rundunar yansanda ta jihar bisa jagorancin kwamishinan Yansanda CP. Sunusi Buba, ta tura jami’an ta na Puff Adder, karkashin Baturen yansanda, na Karamar hukumar Kankara.

Hakan ya biyo bayan samun kiran da suka yi da karfe uku na dare, cewar ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane dauke da bindigogi kirar Ak 47, sun shiga kauyen Gurbi, dake Karamar hukumar ta Kankara, tare da kashe mutum hudu, da kuma satar dabbobi da dama duk da turjiyar da suka samu daga yan bangar kauyen.

Labarai masu alaka:

Yan sanda sun baiwa ‘yan social media horo na musamman

Yan sanda sun kama mai damfarar matasa

Sanarwar ta kara da cewa, bayan samun kiran ne, rundunar ta aike da tawagar ta, bayan musayar wuta tare da taimakon yan banga, suka yi nasarar kashe yan ta’addar goma sha bakwai, tare da kwato shanu guda tamanin 80, da Tumakai dari da takwas 108, da yan ta’addar suka sace daga makotan kauyukan yankin.

Wasu ‘yan ta’adda da harin ya rutsa dasu

A harin da yan ta’addar suka kai sun kashe mutane da suka hada da Alhaji  Sunusi Yar Baka je, da Akilu Isuhu, da Bawa Gidan Mai Ruwa da kuma Nana Hussaini, mai shekaru 25, dake unguwar Farin Dutse, sai kuma Muntari Sama’ila mai shekaru 30, daga kauyen Gidan Korau a Karamar hukumar ta Kankara, inda kuma mutum uku suka samu raunuka.

Sanarwar kuma ta kara da cewa wasu daga cikin yan ta’addar sun gudu da harbin bindiga a jikin su, zuwa yanzu haka, jami’an ‘yansandan na cigaba da fadada bincike a dazukan dake yankin don tabbatar da an cafke wadanda suka gudu, tare da kwace makaman da ke hannun su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!