Labarai
An miƙa ɗaliban St. Mary da aka ceto ga hukumomin Neja

An miƙa ɗaliban nan su ɗari da talatin na makarantar st. mary da aka ceto daga hannun masu garkuwa da su zuwa hannun hukumomi a jihar Neja.
Gwamnan jihar, da wasu manyan jam’ian gwamnati ne suka tarbe su a fadar gwamnati da ke babban birnin jihar Minna bayan da suka iso a motoci shida tare da rakiyar jami’an tsaro.
Hukumomi sun ce an ceto yaran ne yayin wani aiki na musamman da jami’an tsaro suka yi, duk da ba su bayar da karin bayani ba.
Haka kuma mahukuntan sun ce, ɗaliban, da malamai bakwai da aka ceto, su kadai ne suka rage a hannun ƴan bindigar cikin waɗanda aka sace daga makarantar kwana ta Katolika ta St Mary da ke Papiri a watan Nuwamba.
You must be logged in to post a comment Login