Connect with us

Labarai

An nada Alhaji Muslimu Smith a matsayin sabon shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kasa

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Alhaji Muslimu Smith a matsayin sabon shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yansanda ta kasa.

 

Alhaji Muslimu Smith wanda tsohon sufeta janar na ‘yansandan kasar nan ne ya maye gurbin Mike Okiro wanda shima tsohon sufeta janar na ‘yansandan kasar nan ne.

 

Haka zalika shugaban kasar ya kuma nada wasu mutane biyar a matsayin mambobin a hukumar ta kula da ayyukan ‘yansandan.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata wasika da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya karantawa ‘yayan majalisar ya yin zamansu na yau.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,747 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!