Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukumar EFCC zata gurfanar da tsohon gwamnan Kano bisa laifin halatta kudaden haramun

Published

on

A yau ne a ke sa ran hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati zata gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau a gaban babbar kotun tarayya da ke nan Kano bisa laifin halatta kudaden haramun.

 

Rahotanni na nuni da cewa tun a daren jiya ne dai Hukumar ta EFCC ta  tsare Malam Ibrahim Shekarau da kuma tsohon ministan harkokin kasashen ketare Aminu Wali da kuma wani kwamishina a nan jihar Kano Ahmed Mansur.

 

Wata majiya mai karfi a ofishin hukumar ta EFCC a nan Kano ta shaidawa manema labarai cewar wadanda ake tuhumar sun shiga hannun hukumar ne da misalin karfe 9 30 na daren jiya Laraba.

 

Rahotannin sunyi nuni da cewa hayaniya ta kaure a kofar shiga hukumar ta EFCC lokacin da magoya bayan tsohon gwamnan suka yi yunkurin hana shigar da shi ofishin hukumar ta EFCC a daren jiyan.

 

Dubban magoya bayan tsohon gwamnan ne dai suka mamaye titinan da ke sansanin alhazai da ke nan kano, da wasu titinan da ke kusa da hanyar domin nuna adawar su da matakin da EFCC ta dauka na damke Ibrahim shekaru din.

 

Haka kuma kiris ya rage masu zanga-zangar su kwace shi daga hannun jami’an tsaro, lamarin da ya sanya hukumar ta nemi taimakon karin jami’an tsaro domin shigar da shi cikin hukumar.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!