Connect with us

Labarai

An sace yara 1,100 cikin watanni 4 a Najeriya – Amnesty

Published

on

Ƙungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta nuna damuwa kan karuwar sace mutane a Najeriya, inda ta ce an sace akalla mutane 1,100 tsakanin Janairu zuwa Afrilu da muke ciki, musamman a jihohin Arewa.

Daraktan kungiyar a Najeriya, Isa Sanusi, ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa wadanda aka sace na fuskantar mummunan cin zarafi kamar azabtarwa, yunwa, fyaɗe da tilasta su aikata laifi.

Rahoton ya nuna manyan hare-hare a jihohin Borno, Zamfara da Kwara, inda aka sace daruruwan mutane a wurare daban-daban, ciki har da mata da kananan yara.

Amnesty ta bukaci gwamnatin Bola Tinubu da ta gaggauta ɗaukar matakan tsaro domin kare rayuka da dokiyoyin al’umma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!