Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

An samar da kwamitin sauraren korafi zaben kananan hukumomin Kano

Published

on

Bangaren shari’a a jihar Kano ya kafa kwamitin sauraron korafe-korafen zaben kananan hukumomi wanda za’a yi Asabar mai zuwa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in yada labaran babban kotun jihar Kano Baba Jibo Ibrahim.

Sanarwar ta ce kwamitin karbar korafin zaben zayyi zaman sa ne a sakatariyar Audu Bako, inda malam Ahmed Baffa Usman zai kasance Sakataren kwamitin, sai kuma Barista Kabiru Yakasai wanda aka nada a matsayin Mukaddashin sakatare.

A cewar Baba Jibo Ibrahim kafa kwamitin ya yi dai-dai da dokar hukumar zabe ta jihar Kano da aka yiwa gyara ta shekarar dubu biyu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!