Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

A ranar 1 ga watan Maris za’a gurfanan da dan majalisar tarayya daga jihar Kogi

Published

on

A ranar 1 ga watan Maris mai kamawa ne gwamnatin tarayya za ta za ta gurfanar da dan-majalisar tarayya daga Jihar Kogi Sanata Dino Melaye gaban babbar kotun birnin tarayya Abuja, bisa zargin aikata laifuka biyu.

Laifukan sun hadar da bada labarin karya da ya baiwa ‘yan-sanda a cikin watan Afrilun bara, kan yunkurin kashe shi da ya ce an yi, da kuma zargin shugaban ma’aikatan Jihar Kogi Mista Edward Onoja David da ya yin a cewa yana da hannu kan wancan hari da ya ce an kai masa.

Gwamnatin tarayya ta hannun Ministan Shari’a Abubakar Malami ta rubuta zarge-zargen sannan ta shigar gaban mai Shari’a Olasumbo Goodluck na babbar kutun birnin tarayya Abuja da ke Maitaama.

Rahotanni sun nuna cewa labarin da Dino Melaye ya baiwa ‘yan-sanda na cewa an yi yunkurin hallaka shi ba gaskiya ba ne, kuma an jiyoshi yana shaidawa dan tsohon gwamnan Kogi marigayi Abubakar Audu wato Muhammad Abubakar cewa ya shirya hakan ne domin bata sunan shugaban ma’aikatan gwamnatin Jihar ta Kogi Mista Edward Onoja.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!