Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

An samu barkewar cutar amai da gudawa a Borno

Published

on

Gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da barkewar cutar Amai da gudawa ta Cholera, a jihar da mutum 559 suka kamu da cutar.

Kwamishinan lafiya ta jihar, Juliana Bitrus ce ta bayyana haka lokacin da take zantawa da manema labarai a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Juliana Bitrus, ta ce kawo yanzu haka mutum 43 ne suka mutu sakamakon cutar daga cikin wanda suka kamu su 559.

Kwamishinar tace an samu bullar cutar a kananan hukumomin Gwoza da Kaga da Hawul sai Magumeri da Damboa, da Maiduguri da barkewar cutar tafi kamari a yankunan jihar.

Ta kara dacewa gwamnatin jihar na daukar matakan shawo kan cutar, tare da tura jami’an lafiya don killace wanda suka kamu da bada kariya ga sauran mutanen da basu kamu ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!