Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An samu musayar yawu tsakanin masu gabatar da ƙara da Lauyan Muhuyi Magaji

Published

on

An samu musayar yawu tsakanin masu gabatar da ƙara da Lauyan Muhuyi Magaji a zaman kotun na ranar Laraba ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Aminu gabari .

Mai gabatar da ƙara Barista Wada A. Wada ya roƙi kotun da ta basu cikakkun bayanan cika sharuɗɗan belin da aka baiwa Muhuyi Magaji tun da fari.

Nan take Lauyan da ke kareshi Barista Muhammad Ɗan Azumi yayi suka, inda yace ai kwamishinan sharia bashi da ikon wannan bincike

A nan ne kotu ta yanke cewar masu gabatar da ƙara za su iya rubuto takarda zuwa ga magatakarda ko kuma su yi roƙo lokacin da ake gudanar da shari’ar

Hakan yasa kotu ta ɗage zaman zuwa ranar Alhamis gobe 05/05/2022 domin baiwa masu gabatar da ƙara damar rubuto buƙatar su kamar yadda wakilin Freedom Radio Aminu Abdu Bakanoma ya rawaito.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!