Kasuwanci
An samu raguwar hauhawan farashin kayan masarufi a Najeriya- NBS

Hukumar kididdiga ta Najeriya NBS, ta ce, an samu raguwar hauhawan farashin kayan masarufi a fadin kasa da kaso 22.22 cikin 100 idan aka kwatanta da kaso 22.97 cikin 100 a watan Mayun bana.
Rahoton da hukumar ta fitar ya bayyana cewa, idan aka haɗe alkaluman raguwar farashin da aka samu daga farkon shekarar da muke ciki zuwa yanzu, ya ragu da kaso 11.97 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar bara.
Hukumar ta kuma kara da cewa saukin farashin ya fi shafar bangaren kayayyakin abinci da sauran kayan masarufi na yau da kullum.
Tun bayan cire tallafin man fetur ne dai aka shiga cikin matsin rayuwa da hauhawar farashin wanda ya jefa al’ummar Najeriya cikin mawuyacin hali.
You must be logged in to post a comment Login