Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An sanya matakan tsaro a Umuahia, a shirye-shiryen karbar shugaba Buhari

Published

on

Yanzu haka dai an sanya matakan tsaro a Umuahia babban birnin jihar Abia, a shirye-shiryen da gwamnatin jihar ke yi na tarbar shugaban kasa Muhammdu Buhari, da mataimakin sa farfesa Yemi Osinbajo.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaba Buhari da mataimakin sa za su kai ziyara jihar ne, domin halartar taron gangamin jam’iyya mai mulki wato APC, wanda za’a gudanar a filin wasa na jihar da ke Umuahia.

Ana sa ran shugaban jam’iyyar na kasa Chief John Odigie-Oyegun, da shugaban jam’iyyar na kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC Rochas Okorocha, da kuma sauran shugabannin jam’iyyar da ke fadin kasar nan ne zasu halarci taron gangamin.

Sakataren yada labaran jam’iyyar ta APC a jihar Abia Mista Benedict Godson ya bayyanawa manema labarai cewa, sun gama shiryawa tsaf, domin karbar bakuncin shugaba Muhammadu Buhari.

Rahotanni sun bayyana cewa, an baza jami’an tsaro a jihar musamman ma babban birnin jihar, duk domin ganin an gudanar da taron cikin kwanciyar hankali.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!