Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

An siyar da ‘ya ta naira Miliyan Daya da rabi

Published

on

Mahaifin daya daga cikin yaran nan ‘yan jihar Kano da aka sace aka kai su Jihar Anambra, Malam Auwalu Ango ya bayyana cewa bayan an sace ‘yarsa Amira an kai ta Jihar Anambra an kuma siyar da ita akan naira miliyan daya da rabi a jihar Lagos.

Ya ce, a lokacin da jami’an tsaro suka gano yaran tuni an biya naira dubu dari biyar, cikin miliyan daya da rabi da aka siyar da ‘yarsa.

Malam Auwalu Ango ya bada wannan labarin ne a wata tattaunawa da ya yi da Freedom Radio, bayan da rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta yi holen wadanda ake zargi da sace yaran.

Ya kuma bayyana sace ‘yarsa tasa a matsayin kaddara, kasancewar yarinyar ba inda take zuwa daga gida sai makaranta, inda ya ce an sace Amira ne da yamma bayan ta dawo daga makaranta, a lokacin da ta dan fita kofar gida.

Ya ce Amira ta shaida musu cewa su biyu aka sace su a lokacin, inda washe gari aka dauke su aka tafi da su can jihar Anambra.

Malam Auwal Ango ya bayyana farin cikinsa da ganin yar tasa inda ya yabawa jami’an tsaro da irin kokarin da suka yi wajen ganin an ceto yaran.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta dau matakin gaggawa wajen ganin an hukunta wadanda suka sace yaran, inda ya yi kira ga iyaye da su kara sanya ido kan shige da ficen yaran su.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!