Connect with us

Labarai

An tsaurara matakan tsaro a Adamawa gabanin ziyarar Tinubu

Published

on

Rundunar ’yan sanda ta Jihar Adamawa ta kara tsaurara matakan tsaro gabanin ziyarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ake sa ran zai kai jihar ranar Litinin domin kaddamar da manyan ayyukan da Gwamna Ahmadu Fintiri ya aiwatar. Kakakin rundunar, SP Suleiman Yahaya-Nguroje, ya bayyana cewa an sanya rundunar cikin shirin ko-ta-kwana domin tabbatar da zaman lafiya kafin, lokacin da kuma bayan ziyarar shugaban.

 

A cewarsa, Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Dankwambo Morris, ya jagoranci taron tsaro da manyan jami’ai domin duba da kuma kara karfafa matakan tsaro da ake da su. Ya ce an baza jami’an rundunar musamman na sashen sintiri na musamman, yaki da ta’addanci, sa ido na sirri da kuma kula da zirga-zirga a sassa daban-daban na jihar, inda za su gudanar da aikin sa ido cikin sirri.

 

Rundunar ta kuma bayyana cewa za a takaita zirga-zirgar ababen hawa a wasu wurare har sai an kammala bukukuwan kaddamar da ayyukan, tare da tura jami’an binciken bama-bamai domin duba wuraren taro da hanyoyin da za a bi. Rundunar ta bukaci al’umma su hada kai da jami’an tsaro tare da kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!