Labarai
An yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindiga a Mogadishu
Rahotanni daga kasar Somali na cewa an yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da wasu ‘yan bindiga, sa’ao’i kadan bayan mutuwar sama da mutum talatin, sakamakon tashin bom a jikin wani dan kunar bakin wake a babban birnin kasar Mogadishu.
Kamar yadda rahotanni suka nuna harin da ake zargin kungiyar Al-Shabab ta masu tayar da kayar baya ne suka kaddamar, yayi sanadiyyar lalacewar gine-gine da suka hadar da shaguna da kuma wuraren cin abinci.
Tun farko maharani sun mamaye yankunan da suka kaddamar da harin, inda suka fara harbin kan mai uwa dawabi a babban birnin kasar Mogadishi cikin daren jiya zuwa wayewar asubahin yau.
Sama da mutum sittin ne suka samu munanan raunika, yayinda ake cigaba da kwashe fararen hula a wuraren da gine-gine suka rushe, inda ake ganin cewa akwai yiwuwar samun karin adadin mutanen da suka rasa rayukan su sakamakon harin.
A cewar rahotanni har yanzu jami’an tsaro na cigaba da kai komo a wuraren da maharani suka kaddamar da harin, yayinda ake cigaba da binciko wadanda ginin ya rufta a kan su.