Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jami’an tsaro sun kashe wani kasurgumin dan ta’adda da yaransa

Published

on

Rahotanni daga jihar Kebbi, sun bayyana cewa an hallaka wani kasurgumin ɗan bindiga mai suna Yellow, wanda ake zargin shi da yaransa sun addabi yankuna da dama a jihohin Neja da Zamfara da kuma Kebbi.

An dai halaka ja-goran ‘yan bindigan ne da wasu mukarrabansa uku, a wani karon batta da suka yi da jami’an tsaro a garin Wasagu na jihar Kebbi.

A zantawar wakilin Freedom Radio da daya daga cikin kwamandojin mafarautan yankin, ya bayyana cewa, tun farko ‘yan bindigar ne suka kai farmaki gidan wani mutum tare da dauke dansa,sai dai sun samu daukin jami;an tsaro a lokacin inda suka yi ta musayar wuta da bata garin har na fiye da mintina biyar.

Haka kuma ya kara da cewa, bayan kammala musayar wutar ne suka gano gawar kasurgumin dan bindigar tare da yaransa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!