Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An zargi ‘yan jam’iyyar APC da bai wa ‘yan bindiga cin hancin Naira Miliyan 56 don rike daliban Jangebe

Published

on

Tsohon dan takarar gwamna a jihar Zamfara Dr. Sani Abdullah Shinkafi, ya yi zargin cewa, wasu daga cikin jagororin jam’iyyar APC da ke adawa a jihar, sun bai wa ‘yan bindiga kudi da ya kai dala miliyan hamsin da shida suna masu bukatar ‘yan bindigar da su ci gaba da rike ‘yan matan sakandiren Jangebe.

A cewar sa, burin su shine bata sunan gwamna Bello Muhammed Matawalle wajen nuna gazawar gwamnatinsa.

Dr Sani Abdullah Shinkafi wanda ya yi takarar gwamnan jihar ta Zamfara karkashin jam’iyyar APGA a zaben da ya gabata na shekarar dubu biyu da goma sha tara, ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a Gusau babban birnin jihar.

Ya kuma shawarci ‘yan siyasar jihar da su guji yin duk wani abu da zai kara ta’azzara matsalar tsaro da jihar ke fama da ita a wannan lokaci.

Dr Shinkafi ya ce ‘yan siyasar jihar baki daya kamata ya yi su mika wayoyinsu ga jami’an tsaro don ayi binciken kwakwaf akan zargin da ya yi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!