Labarai
Ana ci gaba da yin shirye-shiryen jana’izar Shiekh Dahiru Usman Bauchi

Al’umma daga sassa daban-daban na Najeriya da ma kasashen ketare, na ci gaba da isa garin Bauchi domin halartar jana’izar Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
A yau ne dai za a gudanar da jana’izar tasa Bayan Sallar Jumma’a kamar yadda iyalansa suka bayyana a jiya Alhamis bayan rasuwarsa.
Marigayi Dahiru Usman Bauchi, ya rasu ne da asubahin jiya Alhamis Bayan ya yi fama da rashin Lafiya.
A zantawar wakilimu Abba Isah Muhammad, da Shugaban Sashen kula da Ingancin ayyukan makarantun marigayin watau Malam Dahiru Abubakar Mukutar, ta wayar tarho, ya ce shirye-shirye sun yi nisa wajen binne gawar fitaccen malamin.
You must be logged in to post a comment Login