Labarai
Ana dakon matsayar SWAN kan ƴan sanda bayan hana mambobinta daukar rahoto

Ana dakon matakin da kungiyar manema labaran wasanni ta Najeriya SWAN reshen jihar Kano za ta ɗauka kan matakin hana ‘yan jarida mambobin ta shiga daukar bayanai da jami’an tsaro suka yi jim kadan bayan tashi daga wasan Barau FC, wanda ta yi rashin nasara da ci 1-0 har gida a hannun Warri Wolves a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata.
Hana daukar bayanai dai Laifi ne cikin dokokin hukumar shirya gasar firimiyar Najeriya NPFL , da hakan ka iya jawo hukunci mai tsanani.
A bangare daya kuma ana ci gaba da ce ce kuce dangane da lamarin da kuma waye yake da alhakin aikata hakan tsakanin jami’an tsaron ‘yan sanda , jagororin tawagar ta Barau FC ko kuma hukumar kwallon kafa ta jihar Kano KSFA dangane da hana ‘yan jaridun gudanar da aikin su.
You must be logged in to post a comment Login