Labarai
Ana sa ran El-rufa’i zai amsa gayyatar hukumar EFCC

A yau Litinin ne ake sa ran tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, zai amsa gayyatar hukumar EFCC inda zai bayyana a ofishinta.
Kafar BBC ta ruwaito cewa, El-Rufai ya bayyana a jiya cewar hukumar ta aike masa da takardar gayyata zuwa ofishinta, kuma ya amince zai je ofisihin a yau Litinin.
Wannan lamari dai na zuwa ne bayan rahotonnin da suka bayyana cewa, jami’an tsaro sun ƙwace fasfonsa a Filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe jim kaɗan bayan dawowarsa daga kasar Masar.
Da ya ke yin ƙarin bayani kan wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta, El-Rufai, ya ce ba shi ne ya yi musayar kalamai da jami’an DSS ba, sai dai su ne suka tare shi a filin jirgi suka buƙaci ya bi su ofishinsu.
You must be logged in to post a comment Login