Connect with us

Labarai

Ana Samun yawaitan karuwar kai hare-hare yan bindiga dadi sakamakon makwaftaka da Zamfara

Published

on

Shugaban kwamitin dake kula da al’amuran kwadago da nagartar aiki Sanata Abu Ibrahim ya ce ana samun karuwar yawan kai hare-hare da ‘yan bindiga a jihar Katsina ne sakamakon jihar na makwaftaka da jihar Zamfara.

Da yake ganawa da manema labarai kan karuwar kai hare-hare da ‘yan bindiga ke kaiwa jihar ta Katsina,Sanatan mai wakiltar kudancin Katsina Abu Ibrahim yayi gargadin cewa in har ba’a dauki matakan gaggawa ba wajen shawo kan matsalar, labarin zai sha bam-bam ga sauran jihohin dake arewacin kasar nan.

Haka zalika sanatan ya ce al’ummar jihar Katsina ba za su amince da irin matakin da aka dauka ba wajen shawon kan matsalar ta rashin tsaro a jihar, yana mai cewar yayi imanin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kawo karshen matsalar da take neman addabar jihar ta Katsina.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,749 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!