Connect with us

Labarai

Gwamnan jihar Ondo ya kori kwamishinonin 3 a gwamnatinsa

Published

on

Gwamnan jihar Ondo Oluwarotimi Akeredolu ya sanar da cewar ya kori kwamishinonin 3 dake kunshin gwamnatin sa yayin da nada wasu mutum 5 a matsayin sababbin kwamishinoni.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da sakataren yada labarai ga gwamnan Mr Olusegun Ajiboye ya fitar a birnin Akure.

Sanarwar ta sanar da sunayen sababbin kwamishinonin da gwamnan Akeredolu ya nada sun hada da Mrs Yetunde Adeyanju da Mrs Titilayo Adeyemi da Mr Temitayo Oluwatuyi da  Mr Fatai Olotu da kuma Mr Akindotun

Haka zalika a cewar sanarwar gwamnan jihar ya ce daukar matakin ya zama wajibi wajen yin tankade-da rera, saboda gwamnatin sa na bukatar jajirtattu da za su baiwa jihar ta Ondo gudunmawa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 341,032 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!