Labaran Kano
Ana zargin KAROTA da haddasa hatsari a titin Zariya
Daga Shamsu Dau Abdullahi
Wani hadari mota daya auku a safiyar yau akan titin Zaria Road a nan Kano ya haddasa asarar dukiyoyi da dama baya ga janyo cunkoson ababen hawa wanda ake zargin jami’an hukumar kula da zirga zirga ababen hawa ta jihar kano Karota ne suka yi sanadiyar faruwar al’amarin.
Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa hadarin ya auku ne da misalin daya na daren jiya inda wata mota kirar J5 dauke da goro tayi awon gaba da wata tirela bayan da jami’an hukumar Karota suka tsayar da ita domin bincikarta.
Sun kuma ce ba’a samu asarar rayuka ba sai dai a sarar dukiyoyi mai tarin yawa wanda ya tunzura direbobin tirelan suka rufe hanyar ba shiga ba fita akan titin.
Mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon kazamin hatsarin mota a Kano
Takai:Mutane 19 ne suka rasa rayukansu a wani hatsari da ya afku a kauyen Dinyar Madiga
Ko da muka tuntubi jami’in hulda da jama’a na hukumar Karota Nabilisi Abubakar Kofar Na’isa ya tabbatar da faruwar al’amarin yana mai cewa a yanzu haka tuni hukumar ta fara bincike don daukan mataki na gaba akan jami’an da ake zargin su.
A nasa bangaren shugaban hukumar kare aukuwar hadari ta kasa reshen jihar kano Zubairu Mato cewa yayi sun sami wannan labari ne da safiyar yau shiyasa suka tura jami’ansu domin kawo daidaito akan titin.
Shugaban hukumar yayi kira da direbobi dasu daina tuki wanda ya wuce sa’a a cikin gari dama wajen gari.