Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

APC ta ɗage babban taron ta na ƙasa

Published

on

Jam’iyyar APC mai mulki ta ɗage babban taron ta na ƙasa.

Tun da farko dai jam’iyyar ta tsara gudanar da babban taron ne a ranar 26 ga watan Fabrairun 2022, amma batutuwan da suka haɗa da rikicin shiyya-shiyya da na wasu jihohin sun zama barazana ga taron.

A wata wasika mai ɗauke da kwanan watan 21 ga Fabrairun 2022, shugaban jam’iyyar na rikon kwarya kuma gwamna jihar Yobe Mai Mala Buni, da shugaban kwamitin tsare tsare-tsare na Jam’iyyar Sanata John James Akpanudoedehe ne suka sanar da hukumar zaɓe mai zaman Kanta ta ƙasa INEC batun ɗauke taron.

Sai dai jam’iyyar ba ta sanar da lokacin da za ta yi taron a gaba ba.

Rahotonni na nuna cewa akwai yiwuwar gudanar da taron a watan Maris kamar yadda jaridar Dailytrust ta rawaito.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!