Connect with us

Labarai

APC ta bukaci shugaban INEC ya yi sauyin wajen aiki ga shugaban hukumar na jihar Rivers

Published

on

Jam’iyyar APC ta bukaci shugaban hukumar zabe ta kasa INEC da ya gaggauta sauya wajen aiki ga shugaban hukumar reshen jihar Rivers, Mr. Obo Effanga.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran jam’iyyar, Lanre Issa-Onilu.

Sanarwar ta ce sauya wajen aiki ga kwamishinan zaben na jihar Rivers ya zama wajibi don gudun kar ya fifita jam’iyyar PDP a yayin zaben cike gurbi na gwamnan jihar da za a yi nan gaba.

Lanre Issa-Onilu, ta cikin sanarwar ya kuma ce, suna da kwararan hujjoji da ke nuna cewa gwamnan jihar ta Rivers Nweson Wike, ya hada baki da hukumar INEC wajen nada baturan zabuka na mazabu da na kananan hukumomi wadanda cikakkun mambobin jam’iyyar PDP ne.

A cewar sanarwar tun bayan dakatar da zaben na jihar Rivers, gwamna Nyeson Wike da shugaban hukumar ta INEC a jihar, Obo Effanga, sun zauna a gidan gwamnatin jihar sun rubuta sakamakon zabuka na bogi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!