Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Fadar shugaban kasa:ba’a yi wa Buhari adalci ba kan shuka mara ma’ana kan sake zabe a wasu jihohi

Published

on

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewar, ba’a yi wa shugaban kasa Muhamamdu Buhari adalci ba, kan shuka mara ma’ana da ake wa shugaban kasa Muhamamdu daban-daban kan zaben da za’a sake yi a jihohin da ba’a kammala zabe ba.

Babban mashawarci na mussaman kan kafafan yada labarai Malam Garaba Shehu ne yana bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Malam Garba Shehu na maida maratani kan korafe-korafen da wasu ‘yan jam’iyyar APC suke zaton cewa shugaban Muhamadu Buhari zai yi amfani da karfin mulkin sa  wajen sauya sakamakon zabe a wasu jihohin kasar nan.

Haka zalika Mashwarwacin na shugaban kasa ya gargadi shugabanin siyasa da suke kalaman batanci  yayin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INCE zata gudanar da zabe da bai kammala ba a wasu jihohin kasar nan.

A cewar Garba Shehu wasu tsofafin shugabanin kasar nan kan tsuma baki kan zabe da bai kammala ba, a don hakan ne wasu magoya bayan da ran su ya bacci  suke tunanin cewa  shima shugaban Muhamamdu Buhari na aikata hakan, sai dai shugaban Muhammadu shi na daban ne.

 Ya ce kundin tsarin mulkin kasar nan bai bawa shugabanin kasar nan karfin iko ba, Akan haka ne Garaba Shehu ya bukaci mayo bayan jam’iyyr APC a jihohin da za’a yi zaben da bai kammala ba, da su dage wajen samun kuri’u daga al’ummar dake suke jagoranta,mai makon zaton cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai amfani da karfin sa don amfani da  hukumar zabe don ganin an murde zaben.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!