Labarai
Asalin Sojojin baka a Kano
Bincike ya nuna cewa, sojojin baka wasu mutane da ke shiga kafafen yada labarai don furta kalaman adawa ga abokan hamayyar musamman shirye-shiryen siyasa da nufin kare iyayan gidansu, wanda sau da dama hakan na tunzura abokan adawar tasu mayar da martini marar dadi.
Duk da kowanne dan kasa na da damar fadin albarkacin bakinsa a mulkin Demokaradiyya, hakan yasa wasu mutane da ake kira da sojoin Baka ke shiga kafafen yada labarai don fadin ra’ayoyin mussaaman wajen yin abokan hamayya.
Rahotannin dai sun nuna cewa, wannan lamari na hana wasu mutane shiga kafafen yada labarai suyi Magana dan gudun tsira da mutuncinsu, yayin da kuma ke amfani da damar su.
Tashar freedom Radiyo ta ji ra’ayoyin wasu mazauna birnin Kano kan kalaman batanci da ‘yan-siyasa ke furtawa a tsakanin su, yayin da suke cewa bai da ce, wasu kuma ke cewa ra’ayoyin su, suke bayyanawa.
Akan haka ne muka tuntubi kwararen Dan jarida kuma malami a fannin koyar da aikin Jarida da ke Jami’ar Bayero da ke nan Kano, Dakta Maude Rabi’u Gwadabe, inda ya ce, duk da damar da kundin tsarin mulkin kasar nan, sashe na talatin da tara fadan albarkacin baki, ba daidai bane ‘yan siyasa su riga aibata juna.
Mun kuma ji ta bakin sakataren kungiyar shugaban gidajen rediyo da talabijon masu zaman kansu da ke nan Kano, Nafiu Yahaya, ya ce sun bujiro da hanyoyi da dama don kawo gyara a bangaren.
A nasa bangaren jagoran masu Magana a kafafen yada labarai na Jam’iyyar APC, Habibu Indabawa Mai-Yangu-Yangu, ya ce, har yanzu wasu basu san amfani fadan albarkacin baki ba.
Shi ma sakataren masu Magana a kafafen yada labarai na Jam’iyyar PDP Bashir Sanata, ya ce basa goyon bayan wadanda ke da wancan dabi’a, kuma idan suka fuskanci dan Jam’iyyar su na wuce gona da iri na furta kalaman da basu da dadi ga abokan hammayar su, suna hukunta su.
Al’umma dai na fatan cewa, masu ruwa da tsaki za su yi duk mai yiwuwa wajen kawo gyara a bangaren yayin suke cewa tun a shekarun baya suke yunkurin kawo tsafta cikin wannan aiki.