Labarai
ASUU ta bai wa gwamnatin tarayya mako 2 ta magance matsalolin da ke tsakaninsu

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwana 14 domin magance matsalolin da ke tsakaninsu, ko kuma su fara yajin aikin gargadi na makonni biyu.
Wannan mataki ya biyo bayan taron gaggawa na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (NEC) da aka gudanar a ranar 29 ga Satumba, 2025, inda aka nazarci sakamakon kuri’ar da rassan ASUU suka kada kan batun.
ASUU ta bayyana cewa an riga an sanar da wannan ƙuduri ga Ministan Ƙwadago, Ministan Ilimi, da kuma Kungiyar Ƙwadago ta Najeriya NLC amma har yanzu babu wani ci gaba da ya cancanci a yaba da shi.
Ƙungiyar ta kuma ce, manufar ɗaukar wannan mataki ita ce tilasta wa gwamnati ta cika alkawuran da ta ɗauka tun a watan Faburairu, ciki har da aiwatar da sabunta yarjejeniyar da aka cimma.
Haka kuma ƙungiyar ta yaba wa mambobinta bisa haƙuri da fahimtar da suka nuna, tare da kiran su da su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai da bin umarnin shugabanninsu.
A cewar ASUU, wannan yunkuri ba don wani mutum ɗaya ba ne, sai don kare walwalar malaman jami’a da inganta tsarin jami’o’in Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login