Connect with us

Labarai

Atiku ya bukaci shugaba Tinubu ya ɗauki mataki mai tsauri kan matsalar tsaro

Published

on

Madugun adawa a Najeriya Alhaji Atiku Abubakar, ya bukaci shugaba, Bola Ahmed Tinubu, da ya ɗauki mataki mai tsauri kan matsalar tsaro da ke addabar sassa da dama, ya na mai cewa lokaci ya yi da za a daina surutu a tunkari matsalar a aikace.

 

Atiku ya bayyana haka ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya tuna wa shugaba Tinubu alkawarin da ya yi bayan harin da aka kai a Angwan Rukuba, inda ya ce hakan ba zai sake faruwa ba.

 

Haka kuma, bayyana damuwa kan halin da ake ciki a jihar Nasarawa, inda iyalai ke tserewa da ƙafafunsu sakamakon barazanar hare-hare.

 

Atiku Abubakar, ya jaddada cewa babban aikin gwamnati shi ne kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da inganta walwalar su, don haka ya bukaci shugaban ƙasa da ya tashi tsaye wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da ke addabar Najeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!