Connect with us

Labarai

Ayyukan titunan gwamnatin tarayya zai tallafawa tattalin arzikin kasa – Minista

Published

on

Ministan Ayyuka, Dave Umahi, ya ce manyan ayyukan tituna da gwamnatin tarayya ke gabatarwa zai taimaki ci gaban tattalin arzikin Najeriya.

 

Ya kuma ce an tsara titunan ne domin su dore sama da shekaru 100, yayin da gwamnati ke sauya tsarin daga kwalta zuwa siminti wajen gina hanyoyi.

 

Ministan ya yi wannan bayani ne yayin da yake ganawa da manema labarai a sashen Amansea na titin Onitsha-Awka-Enugu Expressway, bayan duba aikin kilomita 107 da ake ci gaba da yi.

 

Umahi ya jaddada cewa ba za a ci gaba da tsohon salon aiki ba a bangaren gina tituna, yana mai cewa yanzu ana amfani da siminti mai ɗorewa domin tabbatar da inganci da tsawon rai, tare da inganta bunkasar tattalin arzikin yankunan kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!