Connect with us

Labarai

Azabatarwa tayi sanadiyyar tabin hankalin yarinya a Kano.

Published

on

Matashiyar nan da ake zargin mahaifinta ya garkame su da sanya musu sasari  da sarka a kafa tare da dan uwanta wanda rai yayi halin sa a kwanakin baya a garin Rinji dake karamar hukumar Madobi ta gamu da cutar tabin hankali.

Mahifin na su dai yace ya dauki matakin ne saboda taki zaman aure yayin da dan uwanta da ya riga mu gidan gaskiya kuma yake gagara.

Jami’in yada labarai na hukumar hana fataucin bil adam ta kasa shiyyar Kano Aliyu Abba Kalli ya ce saboda halin da ta fada ko Magana bata iya yi kuma ta samu raunin hankali a saboda haka ya zama wajibi su mika ta ga asibitin masu tabin hankali dake nan Kano a Dawanau.

Mutumin da ya daure ‘ya’yan sa shekaru 3 a Kano ya rasu a Asibiti

An gurfanar da uba da ‘yarsa gaban kotu bisa zargin shirya auren bogi

Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya ne babban Kwamandan Hukumar yaki da safarar bil Adama ta kasa NAPTIP shiyyar Kano Shehu Umar ya sanar da cewar mutumin da ake zargi   Malam Muhammadu Ojudi dake  garin Rinji a  karamar hukumar Madobi da laifin daure ‘ya ‘yan sa biyu da sarka da kuma sasari ya rasu  a asibiti  a dai-dai lokacin da ake shirin fara bincikar sa, kan laifin da ya aikata.

Sai dai gabanin rasuwar wanda ake zargi da aikata wannan lamari Muhammadu Ojudi ya bayyana dalilin sa na daukar wannan Mataki na daure yayan nasa guda biyu.

Amma  dai kwamandan Hukumar shiyyar Kano Shehu Umar yace zasu cigaba da fadada bincike kan alamarin duk da rasuwar wanda ake zargi domin gano musabbabin daukar wannan matakin don gujewa musababin faruwar hakan a nan gaba.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,801 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!