Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Azal: Wani mutum ya rataye kansa a Kano

Published

on

Ana zargin wani mutun kai kimamin shekaru 55 a duniya ya rataye kansa.

Da asubahin ranar Laraba aka tarar da mutumin rataye a jikin wata bishiyar darbejiya dake yankin Gaidar makaɗa a ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano.

Wasu shaidun gani da Ido sun bayyana wa Freedom Radio cewa “Mun wayi gari da ganin mutumin sanye da kaya ruwan Madara a jikin reshen bishiyar wuyansa rataye da igiyar ɗinkin buhu wato kirtani sai kuma ƙarin wata wayar chajin waya da ake zargin yayi amfani da su wajen rataye kansa”.

Wakilin Freedom Radio Abba Isah Muhammad yayi ƙoƙarin jin ta bakin Dagacin yankin ƴan kusa a ƙaramar hukumar Kumbotson Malam Bala Isa, Sai dai yace zuwa yanzu suna Asibiti dan haka Sai dai nan gaba zai yi bayani.

Hakan zalika mun tuntubi rundunar ƴansandan Kano Sai dai zuwa yanzu ita ma bata ce komai ba game da faruwar lamarin.

Ku biyo mu a nan gaba don jin yadda ta kasance.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!