Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ba mu fara daukar sabbin ma’aikata ba – DSS

Published

on

Hukumar tsaron sirri ta DSS ta musanta rahoton da ake yadawa cewa tana daukar ma’aikata, kuma ta ce ba ta da wani shafin Facebook a halin yanzu.

Shugaban sashen yada labarai na hukumar Dr. Peter Afunanya ne ya sanar da hakan a Abuja, lokacin da yake musanta wannan rahoto da ake ta yadawa a shafukan sada zumunta na zamani.

Ya ce wani ne mai suna Jesustofunmi Nifemi Alabi ne ya bude shafin Facebook mai suna SSS/DSS Recruitment, domin yaudarar al’ummar da ke kwadayin neman aikin.

Peter Afunanya ya shawarci jama’a da ke neman aiki a DSS da ma sauran bayanai da su duba shafinta na intanet na www.gov.ng don karin bayani.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!