Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Ba mu samu umarnin ƙara farashi ba – Masu ruwan leda a Kano

Published

on

Ƙungiyar masu sayar da ruwan leda da ake kira Pure Water a Kano ta ce, ba ta samu umarnin ƙara farashin kuɗin ruwan ba.

Mai magana da yawun ƙungiyar na biyu Idris Umar ne ya sanar da hakan a zantawarsa da Freedom Radio da safiyar yau Alhamis.

Ya ce, har kawo yanzu babu wani shiri da suke na kara farashin ruwan leda a wannan lokaci, duk da tsadar kayan aiki da suke fuskanta.

Wannan dai ya biyo bayan wata sanarwa da kungiyar masu sayar da ruwan leda ta kasa ta fitar a safiyar yau Alhamis, mai ɗauke da sa hannun shugabar ƙungiyar ta kasa Mrs Clementina Ativie.

Sanarwar da ce, farashin jakar ruwan a yanzu ya tashi daga Naira ɗari biyu da ake sayarwa zuwa ɗari uku a matsayin sabon farashi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!