Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ba ni da hannu cikin zargin damfarar gwamnatin tarayya naira biliyan 51 -Zahra Buhari

Published

on

Daya daga cikin ‘ya’yan shugaban kasa Muhammadu Buhari wato Zahra Buhari ta musanta zargin cewa tana da hannu cikin wata almundahanar kudi naira biliyan 51, har ma aka baiwa gidauniyarta naira biliyan biyu da rabi.

Inda lauyanta Nasiru Aliyu ya bukaci Jaridar nan ta Sahara Reporters da ta wallafa labarin da ta gaggauta janye wa tare da ba da hakuri, sannan ta wallafa ban hakurin a shafukan Jaridun kasar nan guda uku cikin kwanaki bakwai, ko kuma su dauki matakin shari’a.

“Zahra Buhari ‘yar kasa ce ta gari mai bin doka, kuma wannan labari da aka wallafa an yi shi ne don bata mata suna” a cewar Sani Aliyu (SAN).

Jaridar intanet ta Sahara Reporters ce ta wallafa labarin cewa wani jigo a Jam’iyya mai mulkin kasa ta APC mai suna Alhaji Nasiru Danu yana da hannu cikin badakalar kudi da suka kai naira biliyan 51.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!