Connect with us

Labarai

Ba ni ne ba a faifan bidiyon da ake yaɗawa ɗauke da bindiga ba – Ministan tsaro

Published

on

Ministan tsaron ƙasar nan Manjo Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya, ya musanta wani faifan bidiyon da yake yawo a kafafen sada zumunta cewa an ganshi ya shiga jirgi dauke da bindiga kirar AK-47.

Maibaiwa ministan shawara kan kafafen yada labarai Muhammad Abdulkadir ne ya bayyana hakan, ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ce, hotunan da kuma faifan bidiyon labari bashi da tushe ballanta makama, kawai dai masu shirin tada zaune tsaye ne suka kirkire shi.

Muhammad Abdulkadir ya tabbar da cewa, ba za a ƙyale wadanda suka kirkiri bibiyon ba, domin kuwa za a gudanar da bincike domin gano su tare da daukar mataki na gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!