Labarai
Ba sai kun jira umarni ba wajen fatattakar yan ta’adda – Ministan Tsaron Najeriya

Sabon ministan tsaro Janar Christopher Musa ya bukaci ilahirin ma’aikatan da ke karkashinsa masu kaki da fararen hula da su yi amfani da dukkanin matakan da suka dace a yakin da suke yi da ayyukan ta’addanci ba tare da jiran umarni ba.
Christopher Musa ya bayyana hakan ne a jawabin sa na farko bayan isar sa shalkwatar tsaron kasar da ke Abuja a ranar Juma’a.
Musa ya sake nanata alwashinsa na gaggauta daukar matakan da suka kamata wajen murkushe barazanar tsaron da kasar ke fuskanta tare da gabatar da sabbin tsare-tsaren da za su samar da maslaha ga jama’ar kasar.
Tuni dai Janar Christopher Musa ya sanar da wasu sabbin tsare-tsare daga cikin matakan da zai dauka a kokarin yaki da matsalolin tsaron da suka yiwa Najeriya katutu ciki har da janye sojojin da ke shingayen bincike tare da tura su dazuka don tunkarar ‘yan ta’adda.
You must be logged in to post a comment Login