Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ba za mu iya wadatar da Kano da ruwan sha ba -Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, zai yi wahala a samar da ruwan sha a kowane lungu da saƙo na jihar.

Shugaban hukumar bada ruwan sha ta jihar Kano Injiniya Garba Ahmad Ƙofar Wambai ne ya bayyana hakan ga manema labarai yayin ziyarar da mataimakan Gwamna na musamman suka kai hukumar a ranar Talatar nan data gabata.

Ya ce “zai yi wahala a samar da ruwan sha a kowanne lungu da saƙo na jihar ko da kuwa za’a yi amfani da duka kuɗaɗen gwamnati wajen magance matsalar rashin ruwan”.

A cikin dalilan da ya bayar, Ƙofar Wambai ya ce “A saboda girma da faɗaɗa da jihar ke yi a kullum ne ya sanya ba za’a taɓa kawo ƙarshen matsalar ruwan sha ba, duk da a yanzu a iya cewa samun ruwan ya ƙaru da kaso 70 cikin ɗari idan aka kwatanta da shekarun baya”.

Sai dai ya tabbatar da cewa, za su yi duk mai yiwuwa wajen haɓaka harkar bada ruwan shan, har ma a yau Laraba 24 ga watan Nuwamba ne ake sa ran shugaban da daraktocin sa zasu tafi zuwa birnin tarayya Abuja don tattauna batutuwan da suka shafi matsalar ruwan.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!