Labarai
Ba za mu lamunci jan kafa a harkokin shari’a ba- Gwamna Abba Kabir

Gwamnatin jihar Kano ta ce, ba za ta lamunci Jan kafa ba wajen ajiye mutanen da ake tuhuma da laifi a gidan gyaran hali na shekaru fiye da biyar zuwa goma ba tare da yi musu hukunci ba.
Gwamnan Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar zartaswa karo na ashirin da takwas da ya gudana yau Litinin a rukunin gidajen na Shiek Khalifa Isyaka Rabi’u.
Gwamnan, ya kara da cewar abunda ya gani lokacin da suka ziyarci gidajen gyaran hali na Janguza da Goron Dutse inda wadanda ke tsare da ke jiran shari’a ne fiye da masu zaman hukunci.
Don haka ya ce, Gwamnatin Kano za ta hada kai da babbar alkalin-alkalai ta Kano wajen daukar matakin da zai sa a rika yin shari’a cikin lokacin da ya dace.
Yayin taron majalisar zartaswar, Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar Kano da su ci gaba da saka jihar cikin addu’oi’nsu tare da bai wa gwamnati hadin kai yadda ya kamata don ciyar da Kano gaba.
You must be logged in to post a comment Login