Connect with us

Manyan Labarai

Ba za mu shiga tsarin IPPIS ba -ASUU

Published

on

Kungiyar malaman Jamia ta kasa ASUU ta ce bata amince da tsarin nan na biyan albashi na IPPIS ba.
Shugaban kungiyar ta kasa shiyya ta daya dake nan Kano Farfesa Mahmud Lawal ne ya bayyana haka lokacin da yake taron manema labarai  da ya gudana a jamiar Bayero ta Kano
Farfesa Mahmud Lawal yace kungiyar ta Asuu ba zata tsorata da wata barazana ba ta cewar zaa dakatar musu da albashi ba.
Farfesa Mahmud Lawal yace Gwamnatin da ta kasa aiwatar da mafi karancin albashi na tsawon shekara biyar ,ba abar yarda bace .
Daga Nan kungiyar ta malaman jamioi shiyya ta daya ta yi Kira ga Yan Najeriya da kungiyoyi masu zaman kansu da su tilastawa Gwamnatin tarayya da ta samar da tsari da zai inganta tsarin jamioi a Najeriya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 332,922 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!