Labarai
Dagacin garin Kantama yayi Murabus
A jiye Alhamis ne Dagacin garin Kantama dake karamar hukumar Minjibir Alhaji Shehu Galadima yayi murabus daga kujerar sa, bayan da ya shafe shekaru Sittin da hudu 64 yana rike da wannan mukamin.
Dagacin mai shekaru sama da tamanin 80 yayi Murabus ne saboda tsufa ya cimmasa.
Sai dai wata majiya ta bayyana cewar, Alhaji Shehu Galadima yana fargabar cewa kada bayan rasuwar sa za’a iya samun rikici wajen wanda zai gaje shi.
Fadar shugaban kasa tayi magana kan sace hakimin Daura kuma sarkin dogarin Buhari
Gwmantin Kano ta musanta yunkurin sauya wa sarkin Kano Masarauta
Majalisar dokokin jihar Kano ta yadda da kara sarakunan yanka guda hudu
A wata tattaunawa da Freedom Rediyo ta yi shi dagacin ya tabbatar da cewa Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero ya amince da Murabus din na shi kuma ya sahale masa nada ‘Dan shi Alhaji Muhammadu Shehu Galadima a matsanyin wanda zai gaje shi.
Bayan yin murabus din nashi, alummar garin Kantama sun yi dandanzo wajen kai Caffa ga sabon Dagacin.